Masu garkuwa da mutane sun yi garkuwa da sarkin Adara Maiwada Galadima tare da uwar gidan sa a hanyar Kaduna.
Daya daga cikin iyalen Galadima, Ibrahim Yakubu ya sanar da haka wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya inda ya kara da cewa masu garkuwan sun sace basaraken da uwargidan sa ne ranar Juma’a yayin da suke hanyar dawowa daga Kaduna zuwa Kachia.
Yakubu yace masu garkuwan sun tare motar Galadima ne a wani shingen sojoji dake hanyar Idon inda suka harbe dan sandan dake gadin su sannan suka dauke Galadima da matar sa.
” Galadima na tafe ne da direbobin sa biyu,’yar sa daya da jikar sa daya’’.
Har yanzu dai rundunar ‘yan sanda bata ce komai ba game da abin da ya faru.
Discussion about this post