An kashe mutane 55 a rikicin Kasuwar Magani, a Jihar Kaduna -Rahoton ’Yan sanda

0

Kwamishinan ‘Yan sandan Jihar Kaduna, ya bayyana cewa an kashe mutane 55 a kazamin rikicin da aka yi ranar Alhamis, a garin Kasuwan Magani, cikin Karamar Hukumar Kajuru, a jihar Kaduna.

Ahmed Abdur-Rahman ya shaida haka a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a Kaduna, kuma ya ce ‘yan sanda sun kama mutane 22 da ake zargin su na da hannu.

PREMIUM TIMES ta bada labarin yadda gwamnatin jihar Kaduna ta kafa dokar-ta-baci ta ba shiga ba fita a garin Kasuwan Magani.

Kwamishinan ya ce jami’an tsaro sun wanzar da sake zaman lafiya a garin.

Ya ce shi da kan sa ya ziyarci garin ya gana da shugabannin gargajiya, na addini da kuma matasa domin a samu zaman lafiya.

Ya ce za a hukunta dukkan masu hannu a cikin barkewar rikicin.

Shi ma Gwamna Nasir El-Rufai ya roki jama’ar garin su zauna lafiya. Ya kai ziyara ce a ranar Juma’a, kwana daya bayan barkewar rikicin.

Gwamna El-Rufai ya gana da shugabannin kungiyoyin CAN da na Jama’atu Nasril Islam dangane da rikicin.

Kuma ya sha alwashin tabbatar da an hukunta masu hannu a kashe-kashen.

Sai dai kuma a kashe-kashen da aka yi a garin kasuwar magani, a cikin watan Fabrairu, an kama mutane 65 da ke da hannu, amma har yanzu kotu ba ta kai ga yanke musu hukunci ba.

Share.

game da Author