Shugaban hukumar kidaya ta kasa Eze Duruiheoma ya bayyana cewa a lissafin su akwai nakasassu miliyan 19 ke Najeriya.
Ya fadi haka ne a taron bunkasa al’umma da majalisar dinkin duniya ta shirya da aka yi a garin New York kasar Amurka.
Babban Bankin Duniya ya bayyana cewa adadin yawan mutanen dake da nakasa a duniya gaba daya ya kai biliyan daya sannan mutane irin hakan sun fi yawa a kasashen dake ci gaba.
Duruiheoma ya ce a yadda wadannan mutane ke kara yawa a duniya musamman a Najeriya kamata ya yi gwamnatocin kasashen duniya su hada hannu domin kula da wadannan mutane.
” Gwamnatin Najeriya ta tsaro wasu hanyoyi don taimakawa irin wadannan mutane wato nakasassu ta hanyar samar musu da ababen more rayuwa da sana’o’in hannu. Sannan za a horas da su da ma’aikatan gwamnati da suka kusa yin murabus sana’o’in hannu da kuma tsofaffi.
Jami’in ya kara da cewa za a tabbata kowace asibitin gwamnati dake kasar tana yi wa irin wadannan mutane ragi da saukin magani a duk lokacin da suka tafi Asibit.