RIGAKAFI GA YARA KANANA: Muna maraba da wannan shiri – Miyetti Allah

0

A ranar Lahadi ne shugaban kungiyar makiyaya na ‘Miyetti Allah’ reshen jihar Kano Yahaya Madawaki ya bayyana cewa kungiyar na goyan bayan shirin yi wa yara allurar rigakafi.

Ya fadi haka ne da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Makoda dake karamar hukumar Makoda a jihar Kano.

” A yanzu haka akwai wadanda suke ba mu bayanan zuwan masu yi wa yara allurar rigakafi domin mu shirya ‘ya’yan mu kafin su zo. Hakan ya na taimaka mana matuka wajen kare ‘ya’yan mu daga kamuwa da cututtuka matuka.

Bayan haka, yayi kira ga sauran ‘yan uwan sa makiyaya da su rika bari a an yi wa ‘ya’yan su rigakafi da zaran masu yi sun zo. Sannan ya mika godiyar sa a madadin sauran mazauna garuruwan da ke amfana da wannna shiri ga gwamnati bisa wannan kokari da take yi.

Share.

game da Author