GASAR CIN KOFIN NAHIYAR AFRIKA: Najeriya ta lallasa Libya da ci 3 da 2

0

A ci gaba da wasan kwallon fidda kasahen da zasu fafata a wasan kwallon kafa na cin kofin nahiyar Afrika, Najeriya ta doke kasar Libya da ci 3 da biyu.

Wasan dai ya nemi ya canja zani kafin mai bugun gaba na Najeriya Igahalo ya saka kwallo ta 3 a ragar Libya.

Najeriya ce ta fara jefa kwallaye 2 a ragar Libya inda daga bisani kasar Libyan ta ramo su.

Yanzu dai Najeriya ce ke kan gaba a Tebur da maki 9 inda kasar Afrika ta Kudu ke bi mata da maki 8.

Senegal ta doke Sudan da ci daya mai ban haushi.

Share.

game da Author