Rundunar ‘yan sandan jihar Adamawa ta bayyana cewa wasu mahara sun far wa wasu matafiya a hanyar Numan-Kpasham dake kauyen Bali a karamar hukumar Demsa jihar Adamawa.
A dalilin wannan harin mutane biyar sun rasa rayukan su sannan hudu sun ji raunuka.
Kakakin rundunar Othman Abubakar ya sanar da haka wa manema labarai ranar Talata inda ya kara da cewa maharan sun far wa matafiyan ne a hanyar daga Adamawa zuwa Jalingo a daren Litini.
Abubakar ya yi kira ga mutane da su guji daukan fansa ganin cewa rundunar na yin bincike a kai domin kamo wadanda suka aikata wannan laifi.
Bayan haka wani manomi da baya so a fadi sunanan sa ya bayyana cewa wasu matasa ne suka far wa wadannan matafiya a hanyar Numan -Kpasham.
Ya ce matasan sun zargi wadannan matafiya ne da kokarin kai wa kauyen su, Bali hari.
” Sun kashe mutane biyar sannan hudu sun tsira da rauni.
Discussion about this post