Kotu ta daure wasu ’yan Najeriya masu safarar mutane

0

Babbar Kotun Tarayya da ke Benin, Jihar Edo, ta daure wata ‘yar shekara 49, mai suna Ehie Ehirobo tsawon shekara uku a kurkuku, saboda samun ta da aka yi da laifin safarar jama’a.

Wannan bayani na kunshe cikin wata sanarwa da Hukumar Hana Safarar Mutane (NAPTIP) ta buga kuma ta aiko wa PREMIUM TIMES a jiya Talata.

Tun cikin 2011 aka gufanar da ita a kotu inda aka caje ta da tattara mata ana tafiya yin karuwanci da su, yaudarar jama’a da kuma shirya jigilar ‘yan mata su na tafiya karuwanci a kasashnen ketare.

An ce wadda aka daure din ta dauki wata yarinya wadda ta daina zuwa sakandare, ta tura ta wa wajen ‘yar uwar ta mai suna Esther Ehirobo da ke zaune kasar Greece.

Kafin da tafi da ita kasar kuwa, sai da aka kai ta wurin Sarkin Dodanni na Oguname da ke kauyen Isuwa cikin karamr hukumar Orhionmwon, aka sa ta yi rantsuwa da juju.

An ce an aika da fatarin da ta daura ta yi rantsuwar da wasu ababe daga sassan jikin ta zuwa Grecce.

An kai yarinyar kasar Grecce aka saka ta a karuwanci, inda a karshe ta gudu zuwa ofishin jakadancin Najeriya a Greece, daga can aka dawo da ita Najeriya.

Wannan ne ya sa aka daure matar mai safarar yara su na karuwanci, daurin shekaru uku a kotun A.M Liman.

Babbar Kotun Jihar Lagos ma ta daure wani dan jihar Edo mai suna Charles Osagie da aka fi sani da suna Johnson tsawon shekara daya, saboda kama da laifin safarar mutane.

An kama shi ne a kan iyakar Seme, tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Benin, yayin da ya ke kokarin ketarawa da wasu ‘yan mata su takwas.

Share.

game da Author