BULKACHUWA: Yadda shugabannin APC suka yi wa dan takarar sanatan Bauchi wala-wala

0

Duk da cewa tabbatattu kuma rubutattun adadin yawan kuri’un da Usman Tuggar ya samu a zaben takarar fidda gwani na Jam’iyyar APC a mazabar Sanatan Jihar Buachi ta Arewa sun kai 71,508, hakan bai hana shugabannin jam’iyyar na kasa a Abuja cire sunan sa su maye gurbin sa da Mohammed Bulkachuwa ba, wanda ya samu kuri’u 16,680 kacal.

Usman Tuggar da Bulkachuwa na daga cikin ’yan takara biyar da suka fafata a zaben fidda gwanin wanda zai tsaya takarar sanatan da zai wakilci Kananan Hukumomin Bauchi ta Arewa da ta kunshi Itas-Gadau, Zaki, Jama’are, Giade, Gamawa da Shira na Jihar Bauchi.

A karamar hukumar Katagum ne kadai Bulkachuwa ya yi nasara da kuri’u marasa rinjaye, 7,263, shi kuma Tuggar ya samu 6,278. Amma duk sauran kananan hukumomin warwas Bulkachuwa ya sha kasa.

Sauran ‘yan takara kuwa gaba daya babu wanda ya samu ko da jimillar kuri’a 10,000.

Ita kan ta Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta tabbatar da nasarar da Tuggar ya samu a zaben fidda gwanin da aka gudanar.

Daga daga cikin manyan jami’an INEC na jihar Buachi, mai suna Ahmed Waziri tare da sauran jami’ai biyu, Baba Usman da Ibrahim Abdullahi, ne da kan sa ya sa hannu a takardar tabbatar wa Usman Tuggar samun nasarar zaben.

Duk da wannan nasara da Tuggar ya samu, amma sai Shugaban Gudanar da Zabe wanda APC ta tura daga Abuja, mai suna Ahmed Mohammed, ya bayyana sunan wanda ya zo na biyu a matsayin wanda ya yi nasara.

Hakan ne kuma nan da nan ita APC din ta tura wa INEC sunan Bulkachuwa a matsayin wanda ya zo na biyu, duk kuwa da cewa kuri’a 16,680 kacal ya samu. Aka ce ya kayar da wanda ya samu kuri’u 71, 508.

Tuggar ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ya rika zaya ofishin APC a Abuja, amma manyan shugabannin ba su saurare shi ba.

Manyan ’yan siyasa daga Bauchi sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa sun tabbata APC ta ba Bulkachuwa tikitin takara ne domin su amfana da matar sa, Zainab Bulkachuwa, wadda ita ce Shugabar Kotun Daukaka Kara ta Kasa.

“Jam’iyyar APC jam’iyyar ‘yan babakere da karfa-karfa ce kawai. A yi maka rashin adalci idan ka kai kara ko korafi ba wanda zai saurare ka. Wannan rashin kunya ce.” Inji Tuggar.

Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi Kakakin APC, Lanre Issa-Onilu, ya ce ba zai yi magana a kan wani rikici ko wata tankiya guda daya kacal ba, domin har yanzu ba a kammala mika sunayen ‘yan takara ba tukunna.

Ya ce a dan tsahirta masa, zan gaba za su fitar da cikakken sunayen ‘yan takarar APC din gaba dayan su.

Share.

game da Author