Uwargidan gwamnan jihar Neja Amina Bello ta bayyana cewa za ta yi wa mata 50 fidar cutar yoyon fitsari kyauta a jihar.
Amina ta sanar da haka a shafinta na tiwita inda ta kara da cewa ta yi haka ne domin tallafa wa matan dake fama da wannan cuta a kasar nan.
Ta bayyana cewa ba sai lalle an yi wa mace aure da wuri take kamuwa da wannan cuta ba, matsaloli kamar yin nakuda mai tsawo wajen haihuwa, rashin haihuwa a asibiti duk na iya kawo wannan matsalar.
” Na sa an yi wa mata 117 fidar wannan matsalar tare da hadin guiwar likitocin Islamic Medical Association of Nigeria a asibitin Umaru Musa ‘Yar’adu’a dake sabon wuse Abuja, 30 a asibitin Umaru Sanda Ndayako dake Bida, 49 a asibitin Kontagora sannan 10 a asibitin Jummai Babangida dake Minna.
Bayan haka kuma Hajiya Amina ta sa ayi wa mata 206 dake fama da wannan matsalar fida kyauta a wasu jihohin kasar nan.