‘Yan bindiga su kai hari kasuwan dabbobi da rana tsaka a Taraba

0

Wasu ‘Yan bindiga sun far wa kasuwan dabbobi dake garin Mararraban Kunini a karamar hukumar Lau, jihar Taraba.

Wani da abun ya faru a idanuwar sa ya bayyana mana cewa shima da kyar ya tsira da ran sa a wannan hari.

” Maharan sun far wa kasuwar ne a daidai mutane na hadahadar kasuwanci kawai sai wadannan mutane suka fado cikin kasuwar suna harbi ta ko-ina. Nan take wasu ‘yan kasuwa uku suka rasu sannan wasu har 7 sun samu rauni.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar haka inda ta kara da cewa tuni jami’ai sun fantsama domin kamo wadannan ‘yan taratsi.

Idan ba a manta ba a draen Juma’an da ya gabata ne wasu mahara suka far wa wani Kauyen Fulani a Taraba inda suka kashe shanu har 150.

Shima wannan harin ya auku ne cikin dare kuma kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya tabbatar da aukuwar hakan.

Ya ce rundunar sa ta maida hankali don ganin an kamo masu aikata irin wadannan munanan ayyuka a fadin jihar.

Share.

game da Author