An nada Saraki daraktan kamfen na Atiku

0

Jam’iyyar PDP ta bada sanarwar nada Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki a matsayin daraktan yakin neman zaben Atiku Abubakar a takarar shugabancin kasa na zaben 2019.

Kakakin Yada Labaran Jam’iyyar PDP, Kola Ologbondiyan ne ya fitar da wannan sanarwar a yau Talata, cewa Saraki ne daraktan kamfen na jirgin yakin neman zaben Atiku Abubakar.

Saraki na daya daga cikin ‘yan takara 12 da suka tsaya neman kujerar takarar shugaban kasa tare da Atiku a karkashin PDP.

Shugaban Majalisar Dattawa, zai yi aiki tare da sauran daraktocin kamfen da za su kasance a karkashin sa: Akwai Gwamna Aminu Tambuwal, a Arewa maso Yamma, Davida Umahi a Kudu masu Gabas, Gwamna Ibrahim Dankwambo a Arewa maso Gabas, Gwamna Nyesom Wike a Kudu maso Kudu, Gwamna Samuel Ortom a Arewa ta Tsakiya, sai kuma tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayo Fayose da zai jagoranci kamfen a Kudu maso Yamma.

Kabiru Turaki, wanda shi ma ya tsaya takara tare da Atiku ne zai zama mai bada shawara a harkokin shari’a, yayin da Gwamnan Jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel zai jagoranci kwamitin tara kudaden gudummawa.

Share.

game da Author