Majalisar Dokokin Jihar Kano ta kafa kwamitin mambobi bakwai da za su binciki sahihancin bidiyon da aka buga, inda aka nuno gwamnan jihar Abdullahi Ganduje ya na karbar cin hancin daloli.
Bidiyon ya nuno Ganduje na karbar makudan daloli daga hannun wani da aka ce dan kwangila ne.
An kafa kwamitin ne bayan da Dan Majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Warawa, Lawal Madari, ya nemi a kafa kwamitin bincike, kuma Baffa-Babba Dan’Agundi ya goyi bayan sa.
Madari ya yi nuni da cewa ya zama dole majalisar ta yi wannan bincike, domin a samu tabbatar da wanzar da zaman lafiya da ci gaba a jihar Kano.
Da ya ke magana da zauren majalisa, Shugaban Masu Rinjaye, Baffa Dan’Agundi ya roki gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shigar da karar jaridar da ta fallasa bidiyon tukunna.
Ya ce majalisar dokoki ta jiha na da ikon da dokar kasa ta ba ta na binciken irin wannan batutuwa.
Da ya ke magana, Shugaban Majalisar, Kabiru Rurum, ya ce kwamitin su je su yi bincike, kuma su kawo rahoto a cikin wata daya.
Mambobin kwamitin su na karkashin shugabancin Dan’Agundi, sai Labaran Madari da Zubairu Masu. Akwai kuma Garba Gwarmai, Abdulaziz Garba Abubakar Galadima. Mujitaba Aminu shi ne sakataren kwamiti.
Discussion about this post