Asibitin Kelina dake Abuja ya mallaki na’urar fida na zamani

0

Shugaban kula da fannin fida na asibiti mai zaman ‘Kelina’ dake Abuja, Celsus Undie ya bayyana cewa asibitin ta siyo na’urar yin fida na zamani.

Undie ya bayyana haka ne wa manema labarai a Abuja inda ya kara da cewa asibitin ta siya wannan na’ura ne domin inganta aiyukkan asibitin.

” Babban abin farinciki da mallakar wannan na’ura da muka yi shine, yanzu mutum ba sai ya kwana a asibiti ba. Za a iya yi wa mutum aiki sannan na take ya kama gaban sa.

Ya kara da cewa ba za a kara kudin da ake biya ba wai don mallakar wannan na’ura.

Sannan akwai Gidauniyar da muka hannu da domin taimakawa marasa karfi.

A karshe jami’in gidauniyar Abidemi Babatunde ya bayyana cewa daga farkon shekarar nan zuwa yanzu mutane 70 nr suka garzayo ofishin su don neman tallafin gidauniyar.

” Fidar da za a yi wa wadannan mutane sun hada da cutar dajin dake kama’ya’yan maraina, al’aurorin maza da mata da sauran su.”

Share.

game da Author