Ba mu musanya dan takarar gwamnan Sokoto da Tambuwal ba – Shugaban PDP na jihar Sokoto

0

Shugaban jam’iyyar PDP ya karyata rade-radin da ake ta yadawa wai tuni jam’iyyar ta musanya dan takarar gwamnan jihar da gwamna Aminu Tambuwal.

Tun bayan bayyana sakamakon zaben fidda dan takarar shugaban kasa da jam’iyyar PDP ta gudanar a garin Fatakol, wanda tsohon mataimakin shugaban Kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben aka fara rade-radin cewa Tambuwal da shine ya zo na biyu a zaben zai koma ya yi takarar gwamnan jihar.

Ibrahim Milgoma ya ce ba su musanya dan takarar da ya yi nasara a zaben fidda gwani ba na jam’iyyar da kowa ba. ” Mannir Dan-iya, ne har yanzu dan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar PDP.

” Batun da ke ta yayadawa wai jam’iyyar mu ta musanya Dan-Iya da gwamna Tambuwal ba haka bane. Har yanzu shine dan takarar mu a PDP a jihar Sokoto.”

Mannir yayi kira a mutane da ‘ya’yan jam’iyyar PDP na jihar Sokoto da su hada kai don ganin sun sami nasara a zabukan da ke tafe.

Share.

game da Author