BINCIKE: An gano maganin cutar dake nakasa jarirai tun suna cikin uwayen su

0

Likitoci a asibitin yara dake Philadelphia da wasu dake asibitin jami’ar Pennsylvania, Kasar Amurka sun gano maganin cutar dake nakasa yara tun kafin su zo duniya da ake kira ‘Congenital Disease’.

Bayanai sun nuna cewa wannan cutar na kama jariri ne tun yana ciki da haka ke sa yaro ya zo duniya da nakasa. Sannan jariri kan kamu da wannan cutar a dalilin wasu aiyukkan da iyayen su mata ke yi batare da sanin illar su ba.

Jariri kan kamu da wannan cuta ne idan uwarsa na shan taba sigari, ko tana shan giya, rashin cin abincin da ya kamata da sauran su.

Binciken ya kara nuna cewa ‘ya’yan da aka haifa da wannan cutar kan yi fama da cutar dajin dake kama hanta, rashin kaifin kwakwalwa, kumburin kafafuwa da dai sauran su.

Jagorar wannan bincike Kiran Musunuru ta bayyana cewa sun gano wannan maganin ne baya gwada ingancin maganin BE3 a jikin wasu beraye dake da ciki.

” Da muka gwada ‘ya’yan berayen da aka haifa sai muka ga cewa wannan maganin BE3 ya kare ‘ya’yan berayen daga kamuwa da wannan cutar tare da bunkasa garkuwan jikin su.

Musunuru ta ce basu da tabbacin ingancin wannan magani a jikin mutum amma ta yi kira ga mata dake tsakanin shekarun haihuwa da su kula da irin abubuwan da suke yi domin kare ‘ya’yan da za su haifa nan gaba daga cutar.

A karshe ta shawarci mata masu ciki da su rika zuwa asibiti don duba lafiyar su sannan su rika shan maganin Folic Acid don taimaka musu.

Share.

game da Author