Gwamnan jihar Ekiti mai barin gadu, Ayo Fayose ya bayyana cewa bai ji dain nasarar da Atiku ya samu a zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP da aka yi a karshen makon da ya gabata.
Fayose ya ce ya bi sahun gwamnan jihar Ribas ne don ganin gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal ne ya lashe zaben sai kuma hakan bai yiwu ba.
” Wannan sakamako ya bata mini rai matuka. Babban dalili kuwa shine a lokacin da muka jajurce muka kiwata jam’iyyar muka yi hakuri da ita sannan muka tsaya tsayin daka don ganin jam’iyyar ta yi tasiri, wasun mu sun kauce sun rabu da mu sai kawai kuma ace hakan abu ya zama yanzu.
” Idan wasu suna ganin za su hada kai su yi mana yankan baya. Muna nan muna zuba ido domin ganin karshen gudun ruwan su. Sannan zan iya ficewa daga jam’iyyar ma idan har ta kama in yi haka.
Fayose ya ce yanzu dai suna tattaunawa ne a tsakanin su domin ganin yadda komai zai wakana.