Najeriya fa ba ta siyarwa ba ce – Jam’iyyar APC ga Atiku

0

Jam’iyyar APC ta gargadi ‘yan Najeriya da su yi karatun ta natsu bisa ga dan takarar da jam’iyyar PDP ta tsayar da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari, wato Atiku Abubakar a zaben 2019.

Kakakin jam’iyyar APC, Yekini Nabena ne ya bayyana haka a shimfidaddiyar takarda da ya saka wa hannu da ya kunshi sakon taya murna ga Atiku da yi masa tuni cewa Kasa Najeriya fa ba ta siyarwa bace.

” Tabbas ana ikirarin Atiku kasurgumin attajiri ne wanda yake ganin wannan dukiya tasa ko da karfin tsiya za ta siya masa kujerar mulkin Najeriya musammam ganin yadda ake ta yadawa ya yi ruwan daloli a wajen zaben fidda dan takara da aka yi.

” Mu hakan bai dadamu da kasa ba ko kadan domin yunwar sa na dole sai ya mulki Najeriya ba tun yanzu bane ya fito fili. Atiku ya canja jam’iyya har sau uku yana neman haka. Kuma mun sane yunwa sa ba zai haifar wa Najeriya da da mai ido ba.

Sanna kuma Nabena ya yi kira ga mutanen Najeriya da su yi karatun ta natsu su karkato da hankulan su su duba irin shugaban kasar da za su zaba. Wanda shi gaba daya dukiya da arziki ce takamar sa ko kuma shugaban da talakawa ne a zuciyar sa, wanda burin sa ya shimfida kasar nan a tafarkin gaskiya da zai dore.

Share.

game da Author