Babban Mai Shari’a ya ja kunnen lauyoyi kan yi wa shari’u jan-kafa

0

Babban Mai Shari’a na Kasa, Walter Onnoghen, ya ja kunnen lauyoyi su dai na kawo cikas ga kokarin da ake yi wajen kammala shari’u cikin hankari. Onnoghen ya kara da nuna damuwar cewa Kotun Koli cike makil ta ke da tulin shari’un da kafin a kammala su sai nan da shekarar 2021.

Ya ce wannan gargadi ya yi shi ne domin a tabbatar da samun rika kammala shari’u a Kotun Koli a cikin hanzari, ba tare da bata lokaci ba.

Wannan umarni da ya bayar ga lauyoyi da sauran wadanda abin ya shafa, ya ce tilas ne su tabbatar da cewa sun rika yin aiki da ranakun da aka sa domin sauraren kararraki, ba tare da kawo dalilan dage zaman sauraron kara da ba su da wata gamsasshiyar hujjar neman a daga saurare zuwa wata rana ba.

Babban Mai Shari’ar ya yi wannan gargadin ne a cikin wata takarda da kakakin yada labaran sa, Awassam Bassey ya sa wa hannu a yau Litinin.

Ya ce ya nuna damuwar ne bayan ya gano cewa yawan tulin shari’un da ke gaban Kotun Koti sun yi yawan da sai an kai nan da shekarar 2021 kafin a kammala su.

Ya ce bata lokacin da lauyoyi ke yi na daya daga cikin babban dalilin da shari’u ke cushewa a Kotun Koli.

Share.

game da Author