TAMBAYA: Shin akwai auren Mutu’a a Musulunci ko babu? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

0

TAMBAYA: Shin akwai auren Mut’a a musulunci ko babu? Tare da Imam Bello Mai-Iyali

AMSA: Alhamdu lillah, Tsira da Amincin Allah su tabbata ga shugabanmu Annabi Muhammad SAW.

Shi dai auren mutu’ah shi ne mace da namiji su dai-daita akan zama tare (COHABIT) don biyan bukatar sha’awar su, tsawon wani lokaci da suka amince, bisa wani ladan da namijin zai biya ta, kuma su rabu da zarar lokacin yayi. A wannan aure na mutu’ah babu waliyyai, ko shedu, ko saki, Manufar sa kawai shi ne biyan bukata.

Babu shakka aure a musulunci an ginasa ne don ya dawwama din-din-din, an ginasa akan soyyaya, kauna, tausayi da natsuwa ga ma’aurata, kuma don ya haifar da zuriya, ‘ya’ya da jikoki. Kuma musulunci ya inganta mu’amalar aure da dokoki, hukunce-hukunce da ka’idoji masu yawa kamar
gadon juna, kiyaye tsatson iyali, ciyarwa, tufatarwa, saki, iddah, da sauran dokokin da babusu a cikin mutu’ah.

Hakika a farkon musulunci an halattawa sojoji mutu’ah a lokacin yaki, amma fa babu shakka haramcin sa ya tabbata, kuma haramcin har abada lokacin yakin Khaibara da kuma lokacin Hajjin Annabi na ban-kwana.

Imamul Bukhari da Muslim tare da sauran limaman Hadisi sun ruwaito ingantattun hadisai daga Khalifa Ali (RA) cewa lalle Allah da manzon sa sun haramta auren mutu’ah, haramcin har abada.

Lalle auren mutu’ah haramun ne da ingantaccen nassi, duk malaman musulunci sun yi ittifakin haramcin sa da bacin sa.

Allah shi ne mafi sani.

Imam Bello Mai-Iyali, Kaduna.

A turo Tambayoyi a nan: hausa.premiumtimes@gmailcom

Amsoshin Tambayoyin ku

Amsoshin Tambayoyin ku

Share.

game da Author