Kotu ta daure matar da ta kashe ‘yar kishiyar ta jihar Neja

0

A yau Alhamis ne kotu a garin Minna jihar Neja ta yanke wa wata matan aure mai suna Zulai Kabiru mai shekaru 20 hukuncin zama a kurkuku a dalilin kashe ‘yar kishiyar ta ‘yar watanni takwas da haihuwa.

Dan sandan da ya shigar da karar Emmanuel Ogiri ya bayyana a kotun cewa Zulai ta aikata wannan ta’asa ne a gidan da take aure dake kauyen Dan-auta a karamar hukumar Mariga, jihar Neja

Mijin Zulai Kabiru Labbo ne ya shigar da Karar ranar 9 ga wata.

” Labbo ya bayyana mana cewa Zulai ta shayar da wannan ‘ya ruwan fiyafiya saboda kawai sun dan sami rashin jituwa da uwar wannan jaririya.

Alkalin kotun Ramatu Adamu bayan ta saurari wannan bayanai sai ta yanke wa Zulai hukuncin zama a kurkuku kafin a kammala bincike kan abin da ta aikata.

Za a ci gaba da shari’ar ne ranar 6 ga watan Nuwamba.

Share.

game da Author