UNFPA ta hada hannu da gwamnatin jihar Cross Rivers domin kula da matan dake fama da yoyon fitsari a jihar.
Jami’in UNFPA Yakubu Ali ya sanar da haka ranar Alhamis inda ya kara da cewa mata 12,000 kan kamu da cutar duk shekara a Najeriya.
Ali ya bayyana cewa duk da cewa akan kamu da wannan cutar ta hanyar yi wa mata kaciya amma mata sun fi kamuwa da cutar ne idan mace ta sami dogon nakuda wurin haihuwa.
Ya ce a da yana tunani cewa wannan matsalar a yankin arewacin Najeriya ne suka fi yawa amma bincike ya nuna cewa cutar ta yadu a duk fadin kasar ne.
Ya ce rashin sani da talauci na daga cikin matsalolin dake ci musu tuwo a kwarya.
” A dalilin haka mata da dama ke cutuwa saboda gujewa kunya da nuna wariya da ake yi wa masu fama da wannan cutar.
Ali ya ce sun dauki dabaran shiga cikin kauyuka domin gano matan dake fama da wannan cutar a basu magani.
” Bayan haka muna kira ga matan da suka warke daga wannan cutar su koma gida su wayar wa sauran mata kai game da illolin cutar.