Ni ba ‘barawo’ ba ne – Inji Atiku

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya musanta zargi da bata sunan da ake yi masa cewa ya wawuri dukiyar Najeriya a lokacin da ya ke cikin gwamnati.

Atiku na jawabi ne a garin Ado Ekiti lokacin da ya kai wa Gwamna Ayo Fayose ziyasa a ci gaba da fafutikar sa ta neman an tsaida shi takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

Atiku ya ce dukkan zargin da ake yi masa karairayi ne kawai marasa tushe da makamar hujjoji kawai.

Atiku wanda ya rike mataimakin shugaban kasa a tsakanin 1999 zuwa 2007, an kafa masa kwamitinn bincike a Majalisar Dattawa a karkashin Sanata Victor Ndoma-Egba wadda a cikin 2007 ta fitar da rahoton zargin Atiku da wawurar kudaden Hukumar Kula da Kudaden Rarar Ribar Man Fetur PTDF.

Sai dai kuma a ko da yaushe Atiku ya na karyata wannan zargi da cewa kashin kaji ne kawai Obasanjo da mukarraban sa na cikin majalisar dattawa suka shafa masa, domin su hana shi takarar shugabancin kasa a 2007.

A kokarin da Atiku ke yi na zama shugaban kasa kwanan baya ya fice daga APC ya koma jam’iyyar da ya fice daga cikinta a 2014 wato PDP.

Ya shaida wa wakilan zaben ‘yan takara wato wakilai na jihar Ekiti cewa, idan aka hada hannu aka hada kai, to kayar da APC a zaben shugaban kasa na 2019 ba zai yi wahala ba.

Atiku ya shaida musu cewa ya na rike da cikakken kundin kudirorin da za su ceto kasar nan daga halin kaka-ni-ka-yin da ta ke ciki, matsawar aka zabe shi ya zama shugaban Najeriya.

Share.

game da Author