Zan bayyana matsayi na nan ba da dadewa ba, amma ina PDP har yanzu – Shekarau

0

Tsohon Gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, ya musanta ikirarin da kakakin yada labaran sa, Sule Ya’u Sule ya yi cewa ya fice daga PDP.

A cikin wani wata muryar sa da aka rika maimaitawa a gidajen radiyo daban daban na jihar Kano, Shekarau wanda ya na daya cikin ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP, ya ce shi dai har yanzu ya na nan daram a cikin PDP, kuma ya na ci gaba da tuntubar jama’ar sa domin sanin inda aka dosa.

Ya ce dukkan magoya bayan sa sun san shi da al’adar da ya rike wacce kafin ya zartas da wani hukuncin siyasa, sai ya bi su ya tuntube su tukunna.

Daga nan sai ya roki magoya ban sa da su yi hakuri su jira matakin da zai dauka na gaba.

“Jama’a na sane da abin da PDP ke ciki a yanzu a nan jihar Kano. Uwar jam’iyya ta kasa ta bayyana rushe kwamitin zartaswar jiha na jam’iyyar PDP. Mun kalubalanci wannan hukunci na su a kotu saboda ya saba wa dokar PDP. Har yanzu mu na tuntubar juna da shugabannin jam’iyyar a Kano domin sanin matakin da za mu dauka na gaba.”

Jiya ne kakakin sa Sule Ya’u Sule ya shaida wa Sashen Hausa na BBC ficewa Shekarau daga PDP.

Sai dai kuma lokacin da PREMIUM TIMES ta je gidan Sardaunan na Kano an ce zai gana da jama’ar sa inda zai bayyana matsayar sa a yau Laraba.

Share.

game da Author