FARMAKIN ‘YAN SANDA: Sufeto Janar Idris ya ba Edwin Clark hakuri

0

Kakakin Rundunar ‘Yan sanda ta Kasa Jimoh Moshood, ya bayyana cewa Sufeto Janar Ibrahim Idris ya tura wata babbar tawagar manyan jami’an ‘yan sada zuwa gidan Cif Edwin Clark domin a ba shi hakuri dangane da wani farmaki da ‘yan sanda suka kai gidan sa ba bisa umarnin an sa su ba.

Baya ga wannan kuma an ce ‘yan sandan hudu da suka kai farmaki tuni an rigaya an kama su kuma su su na fuskantar bincike da tukuma.

Tuni dai jami’an tsaron suka ce za a hukunta wadanda suka kai farmakin daidai da laifin da suka aikata.

Kafin a tura jami’ai zuwa gidan Edwin Clark domin a ba shi hakuri sai da hukumar ‘yan sanda ta bada sanarwar kama wadanda suka kai farmakin, tare da musanta cewa ba a aika su shiga yin bincike a gidan dattijon ba.

An dai kai farmakin ne a gidan Edwin Clark din da ke cikin Asokoro Abuja.

An ce wadanda suka kai harin sun je ne bisa bincike da farautar wasu bindigogi da tulin harsasai bayan da aka ce an bi sawu, an gano cewa dattijon ya na boye muggan makamai a cikin gidan sa.

Clark mai shekaru 91 a duniya ya taba rike mukamin minista kafin ya yi ritaya. Sannan kuma shi ne kan gaba wajen kare muradin yankin Neja Delta mai arzikin danyen man fetur. Ana yi masa kallon babban na hannun dama kuma ubangidan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Bayan kai farmakin Clark ya ce ba zai daina bayyana ra’ayin sa kan Shugaba Muhammadu Buhari ba wanda shi dama ya ce bai taba goyon bayan Buhari din ba tun da ya shigo fagen siyasa.

Jimoh ya ce Clark ya amshi ban-hakurin da rundunar ‘yan sandan kasa ta yi masa kamar yadda tun farko shi ne ya nemi hukumar ‘yan sandan da ta gaggauta neman afuwa a rubuce daga gare shi.

Daga nan sai ya ce yayin da aka damke ‘yan sandan hudu ana bincike kafin a yanke musu hukunci a yau Laraba ne za a gabatar da wanda ya tsegunta wa ‘yan sanda cewa ana boye makamai a gidan Edwin Clark.

Ya ce za a tara ‘yan jarida a gabatar da mai tsegumin a gaban su domin kowa ya gan shi. Sannan kuma za a gurfanar da shi a kotu.

Share.

game da Author