EU ta raba irin itatuwa 760,000 a jihar Katsina

0

Hadaddiyar kungiyar raya kasashen Turai EU ta raba irin itatuwa 760,000 wa kananan hukumomi bakwai na jihar Katsina.

EU ta yi wannan rabon ne a kananan hukumomin Baure, Mai’adua, Mashi, Daura, Dutsi, Sandamu da Zango ranar Laraba.

Jami’in shirin Chris Udokang ya bayyana cewa manoma dake shirin suka basu irin wadannan itatuwa domin rabawa mutane.

” Sai da muka tabbatar da ingancin wadannan irin daga hannun manoman da suka raine su kafin muka fara rabon.

Ya ce a dalilin wannan shiri an raba rishon girki 35,000, fatanyu 2,800, gorunan banruwa 6,800, buhunan takin zamani 7,000, lita 7000 na maganin feshi, gorunan feshi 1,200 da garmunan Shanu 700, duk an raba wa mazauna wadannan kananan hukumomi.

Bayan haka jami’ar shirin Kate Kanebi ta ce za su yi iya kokarin su wajen ganin wannan shirin ya kai ga sauran kananan hukumomi.

A karshe gwamnan jihar Aminu Masari yace gwamnatin jihar za ta tallafa wa wannan shiri ta hanyar raba wa mutanen kananan hukumomin dake jihar da rishon girki 34,000.

Share.

game da Author