BOKO HARAM: Njeriya za ta maido ‘yan gudun hijira 56,000 daga Nijar

0

Hukumar bada agajin gaggawa na kasa (NEMA) ta bayyana cewa ta kammala shiri tsaf don dawo da ‘yan gudun hijira ‘yan Najeriya 56,000 daga samun mafaka a kasar Nijar.

Shugaban hukumar na shiyyar Arewa Maso Gabas Bashir Garga ya fadi haka a wani zama da hukumar ta yi tare da jami’an tsaro a Maiduguri jihar Barno ranar Laraba.

Garga ya ce wadanda za a dawo da su ‘yan asalin kananan hukumomin Mobbar ne da Abadam.

Ya kuma roki jami’an tsaro dake aiki a jihar da su hada hannu da kungiyoyin bada agaji domin samar wa ‘yan gudun hijira tsaro daga fadawa cikin wani matsalar ganin cewa sun yi fama da haka a baya.

Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar Barno Ahmed Bello ya bayyana cewa rundunar ta kammala shiri tsaf domin ganin an samar wa wadanda za adawo dasu tsaro ta musamman.

Ya kuma ce sun horas da wadanda za su taimaka wajen sassanta kananan rikicin da ka iya bullowa a tsakanin ‘yan gudun hijiran a garuruwan su.

Bello ya kara da cewa za su hada hannu da sarakuna, kungiyoyin ‘yan agaji, da sauran su domin samar da tsaro a yankuna, garuruwa da sansanonin ‘yan gudun hijira.

Share.

game da Author