Shugaban hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kano (SERERA) Ali Bashir ya bayyana cewa mutane tara sun rasa rayukan su sannan wasu biyar sun ji rauni a dalilin ruwa da akayi kamar da bakin kwarya a jihar.
Bashir ya fadi haka ne ranar Laraba da yake hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a garin Kano.
Akalla kananan hukumomi 9 ne suka yi fama da ta’adin da ambaliyar ruwan ya shafa.
” Mutane sama da 4,475 a kananan hukumomi tara dake jihar ya shafa sannan mutane biyar sun rasa rayukan su a kauyen Rimin Gado, uku a Gabasawa da kuma daya a garin Getso kuma duk a karamar hukumar Gwarzo.”
Ya ce da zaran hukumar ta kammala gudanar da bincike za ta gabatar da sakamakon binciken ga gwamnatin jihar Kano.
Discussion about this post