An maida zaman Kotun Karar Zaben Ekiti Zuwa Abuja

0

Kotun Sauraren Karar Zaben Gwamna jihar Ekiti ta koma da zama Abuja, sakamakon barazanar da alkalan da ke sauraren karar da kuma bangarorin biyu ke fuskanta.

Jam’iyyun biyu sun nuna bukatar sauya wa kotun sauraren karar garin zama ne da Babbar Kotun Tarayya ta Ado Ekiti, bayan da magoya baya suka tayar da wani rincimia ranar Litinin da ta gabata, daidai lokacin da aka fara zaman sauraren korafe-korafe.

Dan takatar jam’iyyar PDP, Kolapo Olusola ne ya shigar da karar rashin amincewa da sakamakon da INEC ta bayyyana cewa dan takarar APC, Kayode Fayemi ya kayar da shi a zaben.

Olusola ya na neman kotun ta bayyana shi a matsayin dan takarar da ya yi nasara, domin abokin karawar say a yi magudi, kamar yadda Olusola ya yi zargi.

Lauyoyin bangarorin biyu su ma sun yi ikirarin cewa sun a fuskantar barazana daga abokan hamayya.

Share.

game da Author