Shugaban Hukumar Kididdiga ta Tarayya, Yemi Kale, ya bayyana cewa hukumar za ta fara kididdige adadin matalautan da ke fadin kasar nan daga ranar 27 Ga Satumba.
Shirin kamar yadda Kale ya bayyana da bakin sa, zai gano gejin da kudaden shiga da kuma karfi korashin karfin samun wadatar abinci da nauyin iya ciyar da kai na kowane matalauci.
Haka dai ya furta a wani taron kara wa juna ilmi da hukumar ta shirya a Keffi, jihar Nasarawa, da ke kusa da Abuja.
Ya ce, “za a fara wannan gagarimin aiki a mako mai zuwa, domin mun yi kasaitaccen shirin farawa.”
“Daga makon nan mai zuwa, za mu fara tura kwararrun da mu ka ba horo domin su rika shiga wasu kebantattun gidajen da aka ware su na tantancewa su a fadin kasar nan.”
Wannan aikin inji shi, zai dauki shekara daya cur ana gudanarwa.
“Za a tattara bayanai na iya adadin abincin da mutum ke iya ciyar da kan sa, abinda yake kashewa a kullum, yawan kadarorin sa da kuma yanayin yadda rayuwar sa ta ke, a ma’aunin talauci da rashin wadatar sa.”
Ya ce an fito da shirin ne domin a san takamaiman yawan adadin matalautan Najeriya, ta yadda za a samu daidaito a wurin kididdiga da gamsasshen lisafi ingantacce da gwamnati za ta rika amfani da shi.
Ya yi amanna cewa yin haka zai sa gwamnatin tarayya a kan hanyar samun nasarar ayyukan raya al’umma da ta sa a gaba.