Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta yi kira ga kasashen yankin Afrika kan tsananta yin amfani da dabarun bada tazarar Iyali domin gujewa kara yawa a duniya musamman yadda kasashen yankin ke fama da karancin ababen more rayuwa.
Gidauniyar ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da ta gudanar inda ta gano cewa mutanen yankin kasashen Afrika na kara yawa sannan ga karancin ababen more rayuwa ya sa mutanen yankin na ta yin hijira zuwa kasashen da suka ci gaba.
A dalilin haka ne shugaban gidauniyar Bill Gates ya yi wannan kira yana mai cewa amfani da dabarun bada tazarar iyali hanya ce na da zai taimaka wajen guje wa wadannan matsaloli da kuma hana mata zubar da cikin da ba a so wanda addinai da dokokin kasa suka kyamata.
” Misali a Najeriya mutanen dake kasar a yanzu haka sun kai miliyan 198 sannan bincike ya nuna cewa wannan yawan zai iya ninkawa zuwa 2050.
Bill yace shawo kan wannan matsalar zai yi tasiri idan ana fadakar da mutane game da alfanun bada tazarar iyali.
Ya ce duk da cewa ada ana kokawa da tsadar wannnan magani amma yanzu akawai maganin a ko-ina kuma wasu asibitocin ma kyauta suke bada shi amma duk da haka mutane basu karbi abin hannu bibbiyu ba.
” A yanzu haka shugaban kasar Amurka ya kyamaci amfani da bada tazarar iyali sannan ‘yan darikan Katolika suma ba su yarda da hakan ba, sai dai mu ba za mu karaya ba za mu ci gaba da aikin mu.”
A karshe ya ce za su fi bada karfi wurin ilimantar da mata domin ta wannan hanya ne mata za su iya kiyasce yawan ‘ya’yan da za su haifa domin su iya kula da su yadda ya kamata.
Discussion about this post