Rikici ya barke a garin Jos, da yawa sun rasu

0

A sabuwar rikici da ya barke yau a garin Jos, rundunar ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwan mutane da dama inda wasu da yawa da suka sami rauni aka garzaya da su asibitin koyarwa na jami’ar Bingham dake garin Jos.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Tyope Terna, ya bayyana wa manema labarai cewa tabbas an samu yamutsi a jihar sai dai cikin gaggawa aka baza jami’an ‘yan sanda don kwantar da tarzomar.

” Wasu dauke da bindigogi ne suka far wa mazauna unguwar Rukuba da ke kusa da Otel din Kowa a cikin garin Jos. A dalilin ruwan sama da aka yi da safiyar Juma’a ne, wadannan ‘yan ta’adda suka yi amfani da wannan damar suka far wa mazauna unguwar.

Bayan wannan hari, wasu matasa sun tattare manyan hanyoyin garin Jos suna cewa ” Yau za a yi ta kare”, suna kone-konen tayoyi da sauran su.

Share.

game da Author