A yau Juma’a ne kakakin rundunar sojin sama Ibikunle Daramola ya tabbatar wa PREMIUM TIMES cewa wasu jiragen yaki biyu sun yi karo a sama sannan suka fado a unguwar Katampe, kusa da kubwa da ke Abuja.
Wadannan jirage sun fado ne a daidai suna atisaye domin shirin bukin ranar ba Najeriya ‘yan cin kai.
Wasu da suka isa wurin da jiragen suka fadi sun bayyana wa PREMIUM TIMES cewa sun hango jiragen na ta tangariri a sama.
” Muna tsaye muka hango wadannan jirage na tangariri a sama, daya daga cikin jiragen ya daki dayan sannan gaba dayan su sukayo kasa.
” Mun isa wurin a daidai jiragen sun fada kasa. Daga nan sai muka yi kokarin ceto matuka niragen amma daya nan take ya rasu.
Tuni dai jami’an tsaro da agaji suka garzaya wannan wuri.

05214/28/9/2018/Sumaila Ibrahim/BJO/NAN