Lamido, Saraki da Kwankwaso sun yi ganawar sirri a Bamaina

0

Jiya Alhamis, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi ganawa daban-daban da ‘yan takarar shugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar APC, Bukola Saraki da Rabi’u Kwankwaso a Jigawa.

Sun yi wannan tattaunawa ce a lokacin da ake tirka-tirkar wurin da za a gudanar da taron Gangamin PDP, wanda za a zabi dan takarar shugabancin kasar nan, wanda Lamido din ke a sahun gaba na masu nema.

Shi ma dan takara Attahiru Bafarawa ya je Dutse a jiya Alhamis, amma har lokacin da aka rubuta wannan labari, Bafarawa bai gana da Lamido ba.

Saraki ya gana da Lamido bayan da ya gama ganawa da wakilan jam’iyya, dama kuma ya je ne domin neman goyon baya.

Saraki ya yi takaitacciyar magana da Hausa, inda ya shaida wa shugabannin jam’iyya dalilan sa na neman takara.

Ya ba mutane da dama mamaki, domin da yawa ba su dauka cewa ya iya Hausa ba.

Saraki ya bayyana wa manema labarai cewa bayan zaben fidda-gwani akwai jan aiki na a yi tafiya tare, kuma dama hakan ne ya sa ya kai wa Lamido ziyara a Bamaina.

Shi ma Kwakwaso ya kai wa Lamido ta sa ziyarar a Bamaina. Sai dai ya ce bai samu damar yin doguwar tattaunawa da shi ba. Amma sun sa wani lokacin da za su sake zama.

Share.

game da Author