Tattalin Arzikin Najeriya na fuskantar barazanar sake durkushewa – Kwamitin Emefile

0

Kwamitin Tsara Harkokin Tasarifin Kudade na Kasa, (MPC) ya yin kakkausan gargadin cewa tattalin arzikin Najeriya daf ya ke da sake durkushewa idan babu kyakkyawan tsarin ayyukan tare tsakanin harkar kudaden kasa bangaren tafiyar da yadda ake kashe kudaden.

Kwamitin ya ce ta haka ne kawai za a iya tabbatar da dorewar kananan hanyoyin inganta tattalin arzikin kasar nan.

Kwamitinn ya yi karin hasken cewa a yanzu kalubalen da ci gaban tattalin arzikin kasar nan ke fuskanta sun hada da tsadar kayayyaki, takura wa kudaden ajiyar kasar nan da ke kasashen duniya.

Daga nan sai kwamitin ya bada shawarar matse aljihu wajen tsarin tasarifin hada-hadar kudade ta hanyar kokarin rike matsayin da aka cimma a yanzu ba tare da sakin talalar tattalin arzikin har a bari ya sakwarkwace ba.

Kwamitin ya kuma yi magana akan adadin kudaden da bankuna ke bayarwa lamuni da kuma adadin kason ribar da bankuna ke dora wa masu karbar lamunin ko bashi.

Akwai kuma adadin da sai bankuna na da wadannan kudade ajiye ne za su rika bayar da lamuni na makudan kudade.

Sannan kuma kwamitin ya jaddada cewa matsawar aka tsaurara matakan nan, to za a magance hauwawar tsadar kayayyaki, karancin hannayen jari da jarin kasan a hannayen jama’a, sannan kuma a rika yin azamar kara yawan kudaden asausun ajiyar gwamnatin tarayya na kasashen waje sannan kuma a kara inganta darajar naira a sikelin canji da takardun kudaden kasashen waje, musamman, Dala, fam da kuma Euro.

Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefile ne ya bayyana wadannan dalili da ke neman kawo barazana ga tatalin arziki da kuma hanyoyin da ya kamata a magance barazanar, a wata ganawa da ya yi da manema labarai bayan kammala taron.

Emefiele ya ce yadda tattalin arziki ke tafiya daga watanni 18 zuwa yau, abin kai wa daukin gaggawa ne matuka.

Ya kara da cewa cancak din da aka samu na harkokin kudaden bangaren mai a farkon tsakiyar shekarar 2018 ma ya kara haddada alamomin barazanar.

Wani dalilin kuma shi ne yadda kudaden asusun ajiyar Najeriya da ke waje ya ragu daga dala bilyan 45 da ake da ita ajiye a karshen watan Yuli, 2018 zuwa dala bilyan 44 ya zuwa 201 Ga Satumba, 2018.

Harkokin musayar kudaden ketare ta ragu da kashi 38.34, wato dala bilyan 6 ta ragu a cikin watan Yuli, ba kamar watan Yuni da ya shude ba da aka samu hada-hadar dala bilyan 9.73.

Sai dai kuma a yanzu wannan kwamiti na da kyakkyawan yakinin cewa tashi da farashin danyen man fetur ya yi zuwa dala 80 a kowace ganga daya, za a samu karin karfin tattalin arziki a cikin watanni uku na karshen shekarar 2018.

A lokacin da Najeriya ta yi kasafin 2018 dai, an yi kasafin ne a bisa kowace gangar danyen man fetur na dala 51. Ga shi kuma a yanzu adadin danyen man da ake hakowa a kowace rana ya kai ganga miliyan 2.3.

Share.

game da Author