Aikin tantance wadanda za a dauka aikin Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa da ke gudana a jihar Nassarawa, yayi tsaye cak a jiya Talata, bayan da wani ya yanke jiki ya mutu.
Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadurra na jihar, Olusegun Martin ya tabbatar da mutuwar mai neman aikin, wanda ya ce namiji ne ba mace ba ce.
Sai dai kuma bai bayyana sunan sa ba. Ya ce mamacin ya mutu ne bayan da aka gwada su tseren gudu na tsawon kilomita biyu. Ya yanke jiki ya fadi ya mutu, bayan da ya kammala gudun.
Kwamandan ya ci gaba da cewa bayan da mai neman aikin ya yanke jiki ya fadi, jami’an kula da lafiya daga bangaren FRSC da kuma na sojojin Najeriya sun yi gaggawar kai masa dauki.
Daga nan aka garzaya da shi a asibitin sojoji na Chari Megumeiri, kuma dama a can ake yi wa masu neman aikin atisayen tantance wadanda za a dauka din.
Martins ya ce sai dai kuma mutumin ya mutu ne mintina 30 bayan an kwantar da shi asibiti.
Da ya ke yi wa iyalan sa ta’aziyya, Martin ya ce wannan mutuwa ba za ta dakatar da aikin tantance wadanda za a dauka din ba.
Ranar 25 Ga Satumba ne Hukumar Kare Hadurra ta Kasa ta fasa shirin daukar ma’aikata 4,000 a fadin kasar nan.
Sai dai kuma ya zuwa ranar da aka fara, wadanda suka cika fom na neman aikin sun kai 324,000.
Jama’a da daman a sukar wannan tsari, ganin yadda ake tsawwala biyan kudade ga duk wanda ke neman aikin, alhali kuma mutum 4,000 kawai za a dauka.
Wata majiya ta bayyana wa PREMIUM TIMES HAUSA cewa baya ga biyar kudin fom da ake cikawa a intanet, duk wanda ya je wurin tantancewar sai ya sayi farar singileti da kuma farin takalmin gudu.
Discussion about this post