Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya bayyana cewa gajiyar doguwar tafiya da kuma ayyuka ba dare ba rana ne ya sa shi barci a Zauren Majalisar Dinkin Duniya, a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke jawabi a Majalisar Dinkin Duniya, jiya a birnin New York na Amurka.
Cikin wata takarda da kakakin yada labaran sa, Crusoe Osagie ya sa wa hannu, y ace gwamnan ya gaji likis saboda ayyuka gajiga, kuma kowane dan adam ya san jiki da jini, zai dan so hutu.
Ya nuna rashin jin dadin yadda aka rika nuna hotunan gwamna Obaseki a shafukan intanet ana nuna shi ya na barci a Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce ba wani abu ba ne, shiri ne da kulle-kullen da wasu suka yi, domin su bata wa gwamnan suna.
Kakakin y ace ya kamata yi la’akari da cewa barci fa barawo ne, musamman idan ya samu wanda ya yi aiki kuma ya gaji likis.
Ya ce ya kamata a tuna irin yadda a nan gida Najeriya ba kowane gwamna ne ke aiki tukuru ya na hana idon sa barci kamar gwamnan jihar Edo, Obaseki ba.