A yau Asabar ne tsohon shuagan hukumar EFCC, Nuhu Ribadu ya kaddamar da tsayawa takarar kujerar gwamnan jihar Adamawa.
A dalilin haka, yau babu masaka tsinke a garin Yola inda dubban masoyan sa da magoya bayan jam’iyyar APC suka dunguma zuwa filin jirgin sama da ke Yola domin tarbar gwarzon su kuma jarumin su.
Saukar jirgin sa ke da wuyi sai gabadayan su suka dunguma zuwa ofishin kamfen din sa dake Yola domin ganawa da’ya’yan jam’iyyar da dubban masoyan sa.
Wannan tafiya sai da ya dauke su sama da awa daya kafin su isa ofishin kamfen din sa dake titin Galadima, Yola.
A jawabin da yayi a gaban dubban magoya bayan sa, Ribadou ya ce lokaci yayi da mutanen jihar Adamawa za su fito daga kangin ragwarbababben shugabanci zuwa ga shugabanci nagari.
” Ina tabbatar muku da cewa idan Allah ya bamu mulki a jihar Adamawa toh kakanku ta yanke saka, domin kuwa zamu tabbata mutanen jihar mu sun wadata da lagwadar romon dimokradiyya.
” Tafiyar babu karya a cikin sa kuma tafiya ce da kowa zai yaba sannan kuma kowa ya shaida cewa a karon farko jihar Adamawa ta lula can koli a fagen ci gaba da inganta rayuwar mutanen jihar.
Ribadu ya ce irin tarin jama’ar da ya gani nuni ne cewa lallai ana neman canji nagari a jihar.
A madadin matasan jihar Sadiq Jacob ya bayyana cewa tabbas wannan kokari na Ribadu ya zo a kan gaba matuka domin kuwa shine ya ke da kwarewa da shaidar arzikin da su kawai sun isa kowa ya mara masa baya, kuma matasan jihar na tare da shi.
Discussion about this post