Tsohon shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya yabi shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa tun bayan darewa karagar mulkin Najeriya ya maida hankali wajen saita kasar nan da kuma ceto ta daga halin ragwargwabewar da ta dau hanyar yi.
Ribadu ya bayyana cewa kamar yadda gwamnatin Buhari ta maida hankali wajen yaki da cin hanci da rashawa, haka ake bukatar asamu gwamnoni da za su kamanta haka a jihohin su.
Ribadu ya kara da cewa wadannan na daga cikin dalilan da ya sa ya fito domin takarar zama gwamnan jihar Adamawa domin a yi wa jihar ayyukan ci gaba da ta rasa a gwamnatocin baya.
A ranar Asabar ne dai Ribadu ya bayyana ra’ayin sa na yin takara gwamnan jihar a Inuwar Jam’iyyar APC.
A dalilin haka, yau babu masaka tsinke a garin Yola inda dubban masoyan sa da magoya bayan jam’iyyar APC suka dunguma zuwa filin jirgin sama da ke Yola domin tarbar gwarzon su kuma jarumin su.
Saukar jirgin sa ke da wuyi sai gabadayan su suka dunguma zuwa ofishin kamfen din sa dake Yola domin ganawa da’ya’yan jam’iyyar da dubban masoyan sa.
Wannan tafiya sai da ya dauke su sama da awa daya kafin su isa ofishin kamfen din sa dake titin Galadima, Yola.
A jawabin da yayi a gaban dubban magoya bayan sa, Ribadou ya ce lokaci yayi da mutanen jihar Adamawa za su fito daga kangin ragwarbababben shugabanci zuwa ga shugabanci nagari.
” Ina tabbatar muku da cewa idan Allah ya bamu mulki a jihar Adamawa toh kakanku ta yanke saka, domin kuwa zamu tabbata mutanen jihar mu sun wadata da lagwadar romon dimokradiyya.
” Tafiyar babu karya a cikin sa kuma tafiya ce da kowa zai yaba sannan kuma kowa ya shaida cewa a karon farko jihar Adamawa ta lula can koli a fagen ci gaba da inganta rayuwar mutanen jihar.
Ribadu ya ce irin tarin jama’ar da ya gani nuni ne cewa lallai ana neman canji nagari a jihar.
A madadin matasan jihar Sadiq Jacob ya bayyana cewa tabbas wannan kokari na Ribadu ya zo a kan gaba matuka domin kuwa shine ya ke da kwarewa da shaidar arzikin da su kawai sun isa kowa ya mara masa baya, kuma matasan jihar na tare da shi.