MATASHIYA: “Ina fatan wannan kamfanin jirage da Najeriya za ta kafa, ya samu cikas, kada shirin ya tabbata. Domin rashin tabbatar sa shi ne mafi alheri ga Najeriya.” – Inji Obey Ezekwesile, kwanaki kadan bayan kaddamar da sunan kamfanin jiragen da Ministan Sufuri, Hadi Sirika ya yi a kasar Birtaniya.
Wata biyu da kwana daya kacal bayan Ministan Harkokin Sufuri, Hadi Sirika ya kaddamar da kamfanin sufurin jirage mai suna ‘NIGERIA AIR’, a ranar 18 Ga Yuli, a yau kuma 19 Ga Satumba, Gwamnatin Tarayya ta bada sanarwar dakatar da shirin dungurugum, har sai yadda Allah ya yi.
Dama kuma Hadi Sirika ne ya kaddamar da jirgin a Filin Jirage na Farnborough dake kasar Britaniya, a lokacin da ake wani bikin nuna jirage na duniya.
A yau ma, Sirika ne ya sake bayyana sanarwar tsaida shirin, jim kadan bayan zaman Majalisar Zartaswa ta Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ya gudana a yau Laraba.
Bayan ya yi wannan jawabi ne kuma jim kadan sai aka sake watsa labarin a shafin san na tiwita.
“Ina mai bakin cikin shaida muku cewa Majalisar Zartaswa ta Tarayya ta Dauki wani mataki na dakatar da shirin kafa Kamfanin Jiragen Sama a halin yanzu. Amma kuma dukkan yarjejeniyar da aka kulla ta na nan ba a yanke ba. Mu na godiya ga jama’a da ke goyon bayan mu a kowane lokaci.”
Har zuwa yanzu dai ba a fadi wani dalilin dakatar da wannan kamfanin sufurin jiragen sama ba, a daidai wannan lokaci da ake kan tattaunawa kamfanin da zai kera jiragen.
Ana sa ran wannan shiri zai ci biliyoyin kudade.
Dama kuma tun lokacin da aka rada wa jirgin suna ‘Nigeria Air’, shirin ya sha suka sosai daga ‘yan Najeriya da dama. Akwai ma masu cewa karya ce kawai da kuma yaudara irin ta ‘yan siyasa ganin, cewa sai da zaben 2019 ya karato, sannan aka bijiro da batun kafa jiragen.
Shi dai ‘Nigeria Air’, Hadi Sirika ne ya kaddamar da shi a fatar baki, a bisa yarjejeniyar cewa za a fara zuba jarin na-gani-ina-so har na dala miliyan 8, sannan kuma a samu kamfanoni masu zaman kan su wadanda za su zuba jarin dala miliyan 300 domin kamfanin zirga-zirgar jiragen ya tsaya da gindin sa.
Yarjejeniyar da ta kara bata wa ‘yan Najeriya rai a wancan lokacin, ita ce ba za a fara kawo jiragen ba, har sai nan da watan Disamba, inda za a fara kawo guda 5 kacal, a cikin shekaru biyar masu zuwa kuma, za a ciko saura guda 30.
Da yawan masu sukar shirin sun rika cewa batun duk bulkara ce da kuma shafa-labari-shuni, domin ba abu ba ne mai yiwuwa, ko muma mai iya dorewa.
Cikin wadanda suka rika sukar shirin a lokacin, har da tsohuwar ministar harkokin ilmi a lokacin gwamnatin Olusegun Obasanjo, Oby Ezekwesile.
Ta yi fata da kuma addu’ar cewa kada Allah ya tabbatar da kafuwar wannan kamfanin zirga-zirgar jiragen sama, domin rashin nasarar sa ita ce mafi alheri ga Najeriya. Ta ce babbar asara ce kafa kamfanin jiragen, tmkar watsa kudi a cikin rijiya.
Daga cikin dalilan da Oby ta bayar a lokacin, ta ce Najeriya ba ta da yalwa da wadatar harkokin hada-hadar kasuwancin da za a zuba wadancan makudan kudade a harkar sufurin jirgin sama har a ci riba.
Baya ga wannan kuma, an yi tunanin gwamnatin Buhari za ta farfado da kamfanin sufuri na Nigeria Airways ne, amma maimakon haka, sai ta kafa sabo, alhali ga babbar rigima can ta dabaibaye Nigerian Airways ta albashi da kudaden fansho da garatuti na ma’aikatan ta na bilyoyin kudade da ba a biya su ba.
Ko a wancan lokacin da aka rada wa ‘Nigeria Air’ suna, wasu tsoffin ma’aikatan Nigeria Airways sun sha alwashin cewa wannan ma rainin hankali ne gwamnatin APC ta yi musu, domin da farko alkawari aka yi cewa idan an ci zabe, za a farfado da Nigeria Airways, ba a kafa sabo ba.
Dalili kenan a lokacin har wasu suka yi kurarin cewa sai sun maka gwamnatin tarayya kotu, domin ko dai a biya su hakkokin su na aikin da suka shafe shekaru a karkashin Nigerian Airways su na yi ba a biya su ba, ko kuma a san yadda za a yi da sabon kamfanin da aka kafa.
Yayin da wasu ba’arin talakawa suka rika murna cewa gwamnatin Buhari ta yi abin kwarai, na kafa kamfanin jirage, a matsayin wani abin ci gaba, wasu kuma sun rika sukar shirin, su na cewa harkar jiragen sama dai ta masu kudi da masu mulki ce, ba ta talakawa ba.
Sun yi kiran cewa maimakon a kafa kamfanin jirage, kamata ya yi gwamnatin tarayya ta yi koyi da abin da gwamnatocin baya suka yi, inda aka sayo wadatattun motocin sufuri domin samun sassaucin zirga-zirga a farashi mai rahusa ga talakawa.