Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya, ta gina cibiyar kula da sojojin da suka ji raunuka a fagen fama da wasu wuraren da hadurra ya ritsa da su.
Kamfanin Dillancin Labarai NAN ya ruwaito cewa an gina cibiyar a cikin Asibitin Sojoji na Kaduna, wato 44 Army Reference Hospital.
An gina bangaren ne tare da gudummawar Gwamnatin kasar Jamus, karkashin wata yarjejeniya da aka cimma cikin watan Disamba, 2017.
Ministan Tsaro Mansur Dan-Ali ne ya bude cibiyar a yau Laraba, ya na mai cewa an bude cibitar ne a karkashin shirin bayar da agajin kayan aiki na Jamus, domin kara karfafa sojojin Najeriya.
Ministan wanda Mohammed Garba ya wakilta, ya ce an samar wa cibiyar da kayayyaKin kula da masu raunuka na zamani da ko a wace kasa ana takama da su.
Ita ma Mataimakiyar Jakadan Jamus a Najeriya, Regina Hess, ta jaddada kudirin kasar Jamus na ganin ta yi bakin kokarin ta wajen taimaka wa Najeriya ta kawar da ‘yan ta’addar Boko Haram.