APC ta canja ranakun zaben fidda-gwanin ‘yan takara

0

Jam’iyyar APC mai rike da mulki ta canja ranakun da za ta yi zabukan fidda-gwanin ‘yan takarar ta.

Wata sanarwa da Sakataren Shirye-shiryen jam’iyyar, Emmanuel Ibediro ya saka wa hannu kuma ya raba wa manema labarai a yau Laraba, ya bayyana cewa za a yi zaben fidda-gwanin shugaban kasa a ranar 25 Ga Satumba.

Canjin ranakun dai inji Ibediro, ya samu amincewa daga Kwamitin Zartaswar Jam’iyyar APC na Kasa.

Zaben Fadda-gwanin Shugaban Kasa, ranar 25 Ga Satumba.

Zaben fidda-gwanin gwamnoni, ranar 29 Ga Satumba.

Cikin makonnin da suka gabata ne dai APC ta fitar da jadawalin ranakun da za ta yi zabukan fidda-gwani, wanda hakan ya sa ta fara sayar da fom ga ‘yan takarar mukaman siyasa daban-daban a fadin kasar nan.

An ci gaba da maida fam da ‘yan takara suka cike har zuwa ranar 14 Ga Satumba.

A wancan jadawalin zaben fidda-gwani na farko da aka fitar, an tsara cewa za a yi zaben fidda-gwanin dan takarar shugaban kasa a ranar 20 Ga Satumba, yayin da za a yi na gwamnoni kwanaki biyar bayan an yi na shugaban kasa.

Za a yi zaben ‘yan takara na majalisar dokoki ta jihohi a ranar 6 Ga Oktoba, kwana daya bayan gangamin jam’iyya da za ta yi domin bai wa dan takarar shugaban kasa tuta da kuma jaddada shi a ranar 5 Ga Oktoba.

Share.

game da Author