2019: Yawan ‘yan takara ba zai tarwatsa PDP ba – Shekarau

0

Tsohon ministan ilmi, kuma daya daga cikinn ‘yan takarar sugabancin kasar nan a karkashin jam’iyyar PDP, Malam Ibrahim Shekarau, ya tabbatar da cewa yawar ‘yan takarar da ke nuna tsayawa a zaben 2019 a karkashin PDP, ba zai haifar da rudani a cikin jam’’iyyar ba.

A cikin wata takardar manema labarai da kakakin gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, mai suna Francis Ottah-Agboh ya sa wa hannu, Shekarau ya yi wannan jawabi ne a ranar Lahadi, yayin da kai ziyara ga gwmnan jihar Bayelsa don yi masa ta’aziyyar mutuwar mahaifiyar sa.

Shekarau wanda ya je har garin Sabgama, mahaifar Dickson, inda ake ake zaman makomin, ya ce yawan masu sha’awar tsayawa takara a karkashin PDP, alama ce mai nuni da cewa ana yi wa jam’iyyar kyakkyawan fata nagari.

Daga nan sai abu mafi kyau shi ne yadda za a shirya zaben ba tare da wani rudani kon tankiya ba.

Shekarau ya kara da cewa dadin abin dai dukkan ‘yan takarar su na da tawakkali ga Allah cewa shi ke bada mulki ga wanda ya so, kuma ko ya abin ya ke dai dan takara daya ne kadai za a tsaida.

“Cikin makon da ya gabata ai PDP ta tara dukkan ‘yan takarar ta, mun tattauna da juna a tsakanin mu. Mun nuna cewa mutum daya ne dai kadai zai yi nasara. Daga nan mu kace mun yi amanna duk wanda Allah ya ba, ba za mu yi tankiya da yin Allah ba.”

Shekarau ya samu rakiyar tsohon karamin ministan tsaro. Ronald Oritsejafor.

Gwamna Dickon ya gode wa Shekarau kan wannan ta’aziyya da ya kai masa.

Share.

game da Author