An bayyana cewa Najeriya ta rasa kashi 96 bisa 100 na dazukan ta, kamar yadda Darakta Janar na Gidauniyar Kara Gandun Daji, Muhtari Aminu-Kano ya bayyana.
Ya ce yanzu dajin da ya rage a kasar nan bai wuce fadin kashi 4 bisa 100 ba.
“An tabbatar da cewa a kullum sai kara asarar dazuka da itatuwan da ke ciki wadanda ke kare nu daga abubuwa da dama mu ke yi. don haka akwai bukatar gaggawa ta yin wani namijin kokari domin a kare sauran wadanda suka rage, tare kuma da tashi tsaye haikan ana dasa itatuwa, ba a Lagos kadai ba, har ma a fadin Najeriya
Kamfanin Dillancin Labarai NAN, ya ruwaito Aminu-Kano ya na cewa Gidauniyar Kare Gandun Daji ta Kasa ta fito da wasu hanyoyi na kara yawan duhun itatuwa a cikinn dazukan kasar nan, daga kashi 4 bisa 100 da suka rage zuwa 25 bisa 100, nan da shekaru 30 masu zuwa.
Daga daga cikin hanyoyin kamar yadda ya bayyana, ita ce a daina saran itatuwa sannan kuma a maida hankali wajen dasa itatuwa domin girke-girke da kuma kera kujeru da gadajen katako a ake yi bagatatan a kasar nan.
Discussion about this post