An damke wanda yi wa ‘yar makwabcin sa mai shekaru 13 fyade

0

Wani mutum mai suna Adewale Olakusi, ya shiga hannun ‘yan sanda bayan da aka zarge shi da yi wa ‘yar makwabcin sa, ‘yar shekara 13 fyade.

An damke shi a cikin Ota, da ke karamar hukumar Ado-Odo cikin jihar Ogun.

Kakakin ‘yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da wannan ga manema labarai a ranar Lahadi, kuma ya kara da cewa mahaifin yarinyar da aka yi wa fyaden ne ya kai kara da kan sa a ofishin ‘yan sanda a ranar Asabar da ta gabata.

Ya ce mahaifin ta ya kai kara a ofishin ‘yan sanda da ke Onipanu, inda ya ce Olakusi ya yi wa ‘yar sa fyade, kuma ya gargade ta cewa kada ta kuskura ta shaida wa kowa.

Ya ce ‘yar ta sa ta shaida masa haka, kuma shi da kan sa ya fuskanci yarinyar na fama da laulayi, sannan kuma ba ta sha’awar cin abinci.

Kakakin ya ce an tambayi wanda ake zargi da aikata fyaden, kuma ya amsa laifin sa, amma ya ce ba yin sa ba ne, shaidan ne ya ingiza shi.

Ya kara da cewa an kai yarinyar asibiti inda aka tabbatar da cewa an yi mata fyaden.

Daga nan sai kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmed Iliyasu ya roki jama’a su yi kaffa-kaffa da kuma kara kula da ‘ya’yan su.

Share.

game da Author