Zaben Katsina da Bauchi, Ku bi mu kai tsaye a nan

0

A yau ne ake gudanar da zaben cike gurbi na sanatoci biyu da ka rasa daga jihohin Katsina da Bauchi.

PREMIUM TIMES HAUSA za ta kawo abubuwan da ya kama ta kusa sani tun daga kada kuri’a zuwa bayyana sakamakon Zabe.

JIHAR BAUCHI

‘Yan Takara da za su fafata a zaben sanata a Bauchi.

Lawal Yahaya Gumau (APC); Isah Yuguda (GPN); Haruna Ayuba (ADC); Aminu Tukur (APP) da Usman Hassan (Kowa Party).

Sauran sun hada da Maryam Bargel (SDP); Husseini Umar (NNPP); Usman Chaledi (PDC); da Ladan Salihu (PDP).

Shima tsohon gwamna Isa Yuguda na jam’iyyar GPN ya fito takarar.

Dan takarar jam’iyyar PDP Ladan Salihu da na APC Yahaya Gumau ne ake sa ran data daga cikin su zai yi tasiri, kamar yadda masu hasashen siyasa suka yi.

An fara kirga kuriu a jihar Bauchi.

SAKAMAKON ZABE, Karamar hukumar Kakakin majalisar Wakilai Yakubu Dogara.

ADC – 60
APC -3992
APP – 1557
DA – 24
GPN – 817
KP – 21
MMN -32
MPN – 39
NNPP – 1924
PDC – 152
PDP – 6,646
SDP – 612

SAKAMAKON ZABE DAGA JIHAR BAUCHI

Karamar hukumar Toro

ADC 471

APC 30,658

APP 472

DA 77

PDP 8420

GPN 5,624

Karamar Hukumar Dass

ADC  132
APC  7,432
APP  857
DA   52
GPN  2117
PDP  4028

Karamar Hukumar Kirfi

ADD – 80
APC -11,051
APP 1039
DA 18
PDP 3336
GPN 339

Bauchi Results Announcement

Bauchi Results Announcement

Dan Takarar sanata na Jam’iyyar APC, Lawal Gumau ne ya lashe zaben cike gurbi da aka yi na shiyyar Bauchi ta Kudu.

Ladan Salihu na jam’iyyar PDP ne ya zo na biyu sai tsohon gwamna Isah Yugudu na jam’iyyar GNP ya zo na uku na kuri’u 33,079.

Ga sakamakon zabe

ADC 1754

APC 119,489

APP 11,717

DA 467

GPN 33,079

KP 240

MMN 429

MPN 322

NNPP 22,896

PDC 1,203

PDP 50,256

SDP 3,800

KATSINA

Tuni tun da sanyin safiya aka fara shata filin dagar kokawar nasarar zaben Sanatan Shiyyar Katsina ta Arewa, da aka fi sani da Mazabar Daura, inda Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya fito.

Duk da cewa akwai jam’iyyu da dama da suka fito zaben, amma dai kallo ya fi karkata a tsakanin ‘yan takarar jam’iyyar APC da PDP, wadanda ‘yan gida daya ne.

Kabir Babba Kaita, wani tsohon jami’in hukumar Kwastan, shi ne dan takarar jam’iyyar PDP, yayin da Ahmed Babba Kaita, wanda dan majalisar tarayya ne, shi ne dan takarar jam’iyyar APC.

Kujerar Sanatan ta zama ba kowa a kan ta, tun a ranar 4 Ga Afrilu, bayan Sanata Mustafa Bukar da ke kai ya rasu.

INEC ta aza ranar yau, 11 Ga Agusta, ranar da za a yi zaben cike gurbin na wannan sanata.

Kwamishinan Zabe na Kasa da ke jihar Katsina, Zakari Kazaure ya ce jam’iyyu shida ne suka fito fafara zaben.

‘Yan takarar APC da PDP, gidan su daya, uba daya, amma uwa kowa da ta sa.

Ahmed shi ne dan majalisar tarayya da ke wakiltar Kusada, Ingawa da Karamar Hukumar Kankiya.

Za a kada kuri’a a kananan hukumomi 12 da suka hada da; Daura, Zango, Baure, Sandamu, Mai’adua, Mashi, Ingawa, Mani, Dutsi, Kusada, Bindawa and Kankiya.

– INEC ta ce Shiyyar Daura na da yawan jama’a masu rajista har 855,092, mazabu 128, akwati 1825 sai kuma rumfuna 1577,

– Buhari ba zai samu zuwa yin zabe ba a karon farko tun daga 2014, saboda ya na kasar Ingila ya na hutu.

– Tun karfe 8.10 na safe aka fara tantance masu zabe a rumfar Bakin Kasuwa 1, Gidan mai lamba 006.

– Sai dai kuma jama’a ba su fito kwan su da kwarkwata kamar yadda aka yi tsammani a wannan mazabar ba.

– Jama’ar garin Daura na ta gudanar da harkokin gaban su, kamar ba wani zabe ake yi a garin ba. Sai dai kawai za a iya cewa an kulle manyan kantuna. Amma ‘yan tireda da masu kananan shaguna duk suna gudanar da kasuwancin su.

KATSINA: Uwargidan dan takarar sanata na jam’iyyar PDP Ramatu Kabiru Babba-Kaita ta bayyana wa manema Labarai cewa wasu na bin masu zabe suna basu kudi don su zabi wadanda suke so.

Ta koka cewa hakan bai dace ba, cewa ya kamata a bari mutane su zabi wadanda suke so ba abi su ana cika musu aljihu ba.

Sai dai kuma shugaban hukumar tsaro na ‘Civil Defence’ ya ce komai na tafiya yadda ya kamata, cikin natsuwa da kwanciyan hankali.

SAKAMAKON ZABE

JIHAR KATSINA

Sakamakon zabe da aka bayyana zuwa yanzu sun nuna cewa dan takarar jam’iyyar APC Ahmad Babba-Kaita ne ke kan gaba inda ya sami kuri’u 55, 974, wan sa da ke takara a jam’iyyar PDP Kabiru Babba- Kaita na da kuri’u 11, 768.

An bayyana sakamakon zaben Kananan hukumomin Dutsi, Daura da Sandamu.

Ahmad Babba-Kaita ya doke Kabiru Babba-Kaita

Dan takarar kujerar Sanata na jam’iyyar APC, Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben cike gurbi da aka gudanar ranara Asabar a Katsina.

Kamar yadda aka bayyana sakamakon, Ahmad Babba-Kaita ya sami kuri’u 224,607 sannan Wan sa, da tsohon ma’aikacin kwastam ne, kuma dan takara na jam’iyyar PDP Kabir Babba-Kaita ya sami kuri’u 59,724.

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta bayyana cewa cikin mutane 855,092 da suka yi rijista, sama da mutane 300,000 ne aka tantance a rumfunar zabe dake wannan shiyya.

Share.

game da Author