Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki da Mataimakin sa, Ike Ekweremadu, sun zargi gadar shugaban kasa cewa ta na kokarin kulla musu sharrrin cewa su ne su ka dauki nauyin SSS suka mamaye Majalisar Tarayya.
A wata takardar manema labarai a ofisoshin su biyun suka sa wa hannu, sun ce sharrin har ma ana kokarin hadawa da wasu sanatocin jam’iyyar PDP.
Yusuph Olaniyonu da Uche Anichukwu, wadanda su ne kakakin Saraki da Ekweremadu, sun rattaba cewa fadar shugaban kasa ta kafa wani kwamitin bincike wanda zai duba rahoton da Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Idris Ibrahim ya gabatar.
Sun ce rahoton da kwamitin ke hadawa na kokarin dora musu sharri ko shafa musu kashin kaji cewa su ne suka umarci SSS su mamaye majalisar.
Rahoton na Sufeto Janar Idris dai ya ce SSS sun yi wa wasu ‘yan siyasa cika-aiki ne, amma bai bayyana ko su wane ‘yan siyasar ba.
Rahoton na Idris ya bayyana cewa SSS sun kai mamayar ce ba tare da sanin sa a matsayin sa na Sufeto Janar na ‘yan sanda ba.
Idan ba a manta ba, Saraki a taron da ya yi da manema labarai, ya ce masu cewa shi ne ya dauki nauyin SSS, su na raina wa ‘yan Najeriya wayau kawai.
Sanarwar ta yau ta su ta yau Juma’a ta ce aikin da aka ba kwamitin shi ne su birkita gaskiya, su maida ta karya, ta hanyar dora musu laifin mamayar da SSS suka kai Majalisar Tarayya.