Gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha ya bada hutun kwanaki biyu wato ranar Laraba 15 da Alhamis 16 ga watan Agusta domin mazauna da ‘yan jihar su karba da yin rijistan katin zaben su.
Okorocha ya bayyana bada wannan sanarwa ne da yake ganawa da manema Labarai a garin Owerri.
” Bayanai sun nuna cewa wannan jiha ta mu na daya daga cikin jihohi a kasar nan da mutane suka ki karbar katin zaben su, wasu ma basu yi bama. Saboda haka ba za a bude kasuwa ba kuma ba bu aiki ranar. Kowa ya je ya yayi katin zabe.
” Ina tabbatar muku da cewa canza shekar da wasu cikin mu suka yi zuwa wasu jam’iyyu abin alheri. Ra’ayin su suka bi.