‘Yan gudun hijira sama da 5000 sun koma garuruwan su a Zamfara

0

A yau Laraba ne shugaban Operation ‘Sharan Daji’ a jihar Zamfara Muhammad Muhammad ya bayyana cewa rundunar ta sami nasarar maida ‘yan gudun hijira sama da 5,000 garuruwan su a jihar.

Ya fadi haka ne a haka ne wa manema labarai a garin Gusau sannan ya kara da cewa wadanda aka maida sun hada da wadanda ke kauyukan Galadi, Kwaddi da Katuru dake kananan hukumomin Zurmi da Shinkafi.

Bayan haka kuma a dalilin wuta da muka bude wa wadannan taratsi ne ya sa a yanzu manoma a karamar hukumar Maradun, jihar Zamfara sun koma gona.

” Idan baku manta ba mun fara wannan aiki ne a ranar 1 ga watan Yuli inda a yanzu haka mun kama da dama daga cikin su sannan za kuma mu ci gaba da farautar sauran a cikin dazukan Zamfara.

Bayanai sun nuna cewa Muhammed Muhammed zai ajiye aikin shugabancin wannan rundunar sannan zai mikawa na biye da shi Stevenson Olabanji shugabancin rundunar.

Share.

game da Author