Kwastam ta kama mota dankare da buhunan Wiwi da wasu dauke da kwalaben Kodin

0

Shugaban hukumar kwastam na jihar Legas Mohammed Uba ya bayyana cewa hukumar sa ta kama babban mota dankare da buhunan ganyen tabar wiwi.

Ya fadi haka ne ranar Laraba yayin da yake ganawa da manema labarai a legas.

Uba ya bayyana cewa sun kama wannan mota kirar Ford a hanayar Olorunda jihar Ogun a makon da ta gabata.

Ya ce masu safara wiwidin sun boye buhunan ta ne a karkashin kwandunan tumatiri.

Ya ce za su danka wa hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike a kan su.

Bayan haka Uba ya kara bayyana cewa a cikin wannan makon hukumar ta kama wata babbar mota dauke da kwalaben maganin kodin da ya kai 2,748 da kwalayen maganin ‘Chaka Pain Xtra’ guda 95.

Ya ce a lissafe kudaden wadannan magunguna da suka kama zai kai Naira biliyan 1,175,200,000.

A karshe Uba yace hukumar ta kama buhunan fatar wata dabba da ake kira ‘Pangolin’ da turanci 21, kahon giwa hudu da ya kai nauyin kilo garam 29.35 da motoci masu kira daban daban da gwamnatin kasar nan ta hana shigowa da su a wani gidan ajiyan kaya dake Victoria Island a Legas.

Ya ce wasu cikin mutanen da suke da alaka da shigowa da wadannan kayan sun gudu amma hukumar ta sami nasaran kama mutane takwas daga cikin su.

Share.

game da Author