Ba mu harbi direbobin da suka yi zanga-zanga a Abuja ba –’Yan sanda

0

Rundunar ‘Yan sandan Babban Birnin Tarayya, Abuja, ta bayyyana cewa babu wani dan sandan da ya yi harbi a inda dandazon direbobin manyan motoci suka gudanar da zanga-zanga a kauyen Dabi, cikin Karamar Hukumar Kwali, Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN, ya ruwaito cewa zanga-zanga ta barke yayin da wasu ‘yan sanda suka bude wa wata motar daukar kaya, mallakar kamfanin Dangote, har suka ratattaka wa motar taya.

An kuma ruwaito cewa sun kara harbin tayar wata motar, wadda ta tare hanya, domin nuna fushin bude wa motar kamfanin Dangote wuta da ‘yan sandan suka yi.

Sai dai kuma kakakin yada labaran ‘Yan sanda, Mamzah Anjuguri, ya shaida wa NAN cewa, “yan sanda ba su yi harbi ko daya a wurin zanga-zangar ba.

Ya kara da cewa an bude hanya, bayan da Kwamandan Shiyyar Gwagwalada da Kwali ya sa baki a wurin masu zanga-zangar.

Share.

game da Author